Rundunar ‘yan sandan kasa NPF ta tabbatar da cewa mutune 22 ne suka mutu a turmutsutsun karÉ“ar tallafin abincin da ya faru a garin Okija na jihar Anambra.
Rundunar ta gargaÉ—i duk masu shirya rabon tallafin abinci makamancin wanda ya halaka al’ummar da su sanar da ita kafin aiwatarwa, don hana afkuwar irin haka.
Zuwa yanzu dai mutane 57, aka tabbatar sun mutu sakamakon turmutsutsun karɓar tallafin abincin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara a jihohin Anambra, Oyo da birnin tarayya Abuja.