Rundunar ‘yan sandan kasa NPF ta tabbatar da cewa mutune 22 ne suka mutu a turmutsutsun karÉ“ar tallafin abincin da ya faru a garin Okija na jihar Anambra.
Rundunar ta gargaÉ—i duk masu shirya rabon tallafin abinci makamancin wanda ya halaka al’ummar da su sanar da ita kafin aiwatarwa, don hana afkuwar irin haka.
A jiya Asabar ne wannan abu ya afku, lokacin da wata gidauniya ke rabon kayan masarufi na bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara da suka hadar da shinkafa, da man girki ga talakawa.
A dai jiyan asabar a Abuja mutum 10 ne suka mutu sakamakon makamancin wannan turmutsutsun karÉ“ar tallafin abinci daya faru a wata majami’a da ke unguwar Maitama.
Wannan iftila’i na mutuwar mutane yayin karbar tallafin abincin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara ya faro daga birnin Ibadan na jihar Oyo, wanda turmutsutsun yayi sanadiyyar mutuwar kananun yara 35.
A jiya ne aka ji wata sanarwa daga shugaban Nigeria Tinubu, inda ya jajantawa iyalan mamatan.
Zuwa yanzu dai ba’a ji wani mataki da gwamnati ta shirya dauka ba, don saukakawa al’umma kuncin rayuwa da ake ciki, bisa hujjar cewa shine sanadiyyar rasuwar mutanen, wanda ba’a taba fuskantar irin sa ba a tarihi.