Shugaban Nigeria Tinubu, yace ko kadan bai taba jin nadamar cire tallafin man fetur da yayi ba tun farkon ranar daya karbi mulkin kasar.
Shugaban, ya sanar da hakan a lokacin da manema labarai ke tattaunawa dashi akan yanayin tafiyar da al’amuran gwamnatin sa kusan watanni 19.
Yace, kamata yayi a bar shi ya nuna kwarewar da yake da ita wajen shugabantar Nigeria, ba kalubalantar manufofin sa ba.