Bata gari sun farmaki fadar Etsu Nupe dake Lokoja

0
65

Wasu bata gari da ake kyautata zaton cewa yan daba ne sun kai hari fadar Etsu Nupe dake Lokoja, Emannuel Akamisoko Dauda-Sekila, Nyamkpa, inda suka lalata motoci da sauran abubuwan amfani na masarautar.

Rahotanni daga masarautar sun bayyana cewa an kai harin da misalin karfe 1 da dare asabar data gabata, amma basaraken ya tsallake rijiya da baya.

Sarkin yace bugun kofofin fadarsa da maharan suka yi ne ya tashe shi daga barci, tare da neman tsira da rayuwar sa.

Basaraken ya bukaci gwamnati da jami’an tsaro su bincika lamarin tare da hukunta masu hannu a ciki.

Ya kuma yi kira ga ga al’ummar Nupawa mazauna garin Lokoja da suka kasance masu bin doka kada su dauki doka a hannunsu da sunan ramuwar gayya ko makamancinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here