Hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC tace cutar zazzabin Lassa ta kama mutane 1,154, a Nigeria yayin da 190 daga cikin su suka mutu daga farkon shekarar 2024 zuwa yanzu.
Shugaban hukumar Dr. Jide Idris, ne ya sanar da hakan a yau litinin, lokacin da yake bayyana abubuwan da suka shafi barkewar cutar a birnin tarayya Abuja.
Yace mutane 9,492, ake zaton sun kamu inda aka tabbatar da harbuwar 1,154, sannan 190 suka mutu.
Shugaban ya kara da cewa jihar Ondo tana da kaso 29 na masu cutar sai Edo mai kaso 22, Bauchi kaso 17, Taraba 8, Benue 5, sai Ebonyi mai kaso 4.