Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun kirsimeti

0
27
Tinubu
Tinubu

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun laraba da alhamis 25-26 na watan Disamba a matsayin ranakun bukukuwan kirsimeti.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar a yau Litinin.

Tunji-Ojo ya miƙa sakon taya murnar kirsimeti ga ƴan Najeriya, sannan ya nemi a yi amfani da lokacin bukukuwan domin nuna ƙauna da zaman lafiya.

Ya ce gwamnatin Nigeria a shirye take wajen cigaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaro da ci gaban ƙasa, sannan ya taya kiristoci murna, tare da fatan alheri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here