Saka doka akan bayar da tallafi zai rage taimako—Peter Obi

0
28

Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar LP Peter Obi, yace sakawa masu son bayar da tallafin kayan abinci doka zai iya rage yawan bayar da tallafin musamman a yanzu da al’umma ke cikin kuncin rayuwa

Kalaman Obi, sun zo bayan da sufeta Janar na yan sandan kasa Egbetokun, ya sanar da cewa akwai bukatar masu son raba tallafin su rika Tuntubar jami’an tsaro, gabanin rabon tallafin, da kuma bin sharadin kaucewa jikkata ko rasa rayukan mutane.

Egbetokun, ya bayyana hakan ne bayan turmutsutsu a wajen rabon tallafi ya jawo asarar rayuwa da dama wanda Obi ya ce hakan zai sa gwiwar mutane ta yi sanyi wajen taimakon al’umma.

Jaridar Daily trust, ta rawaito cewa akalla mutane 72 ne suka mutu cikin makon daya gabata sakamakon turmutsutsun karɓar tallafin abinci.

Sai dai tuni fadar shugaban kasa tace Peter Obi, yana yin amfani da kalubalen da yan Nigeria ke ciki don neman yardar su a fannin siyasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here