Gwamnatin tarayya ta wanke mutane 888 da ake zargi da ta’addanci

0
34

Gwamnatin Nigeria ta wanke Mutane 888 wanda ake zargin suna da hannu a ayyukan ta’addanci, inda gwamnatin tace an kasa samun hujjojin da zasu tabbatar da cewa mutanen yan ta’adda ne.

An gudanar da yin afuwar a jiya litinin lokacin da aka gudanar da zaman shari’ar mayaƙan boko haram da sauran masu alaƙa da ƙungiyar wanda cibiyar yaƙi da ta’addanci ƙarƙashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro ta gudanar.

:::Miji ya kashe matar sa saboda rikici akan dafa Doyar da zasu ci

Yin afuwar ya kunshi mutanen da suka jima a daure sakamakon zargin su da laifin shiga kungiyar Boko Haram.

A zaman shari’ar mutane dubu 1 da 743 ne suka gurfana inda a zaman na jiya aka bankaɗo wasu mutane 200 da aka tabbatar da alaƙarsu da ƙungiyoyin ta’addanci.

Bayanai sun ce a tsakanin shekarar 2017 zuwa 2024 mutane 742 aka yankewa hukunci, yayin da da kotu ta wanke 888, sai kuma mutane 92 da aka ɗage shari’arsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here