Miji ya kashe matar sa saboda rikici akan dafa Doyar da zasu ci

0
46

Wani mutum yayi sanadiyyar mutuwar matar sa bayan da rikici ya shiga tsakanin su akan doya.

Lamarin ya faru a jihar Ebonyi, tsakanin mijin mai suna Joshua Nwafor, da mai dakin sa Charity.

:::Sai tsohon kayan mu ya kare zamu rage farashin fetur—IPMAN, NNPCL

Ma’auratan sun shafe akallla shekaru 17, a tare, wanda rabuwar su tazo ta hanyar kisa akan sabanin yadda za’a sarrafa doyar da mai gidan ya siyo.

Bisa ga yadda bayanai suka nuna Charity, tana son a soya doyar yayin da shi kuma Joshua, ke son a dafa ba tare da soyawa ba.

  • Ana tsaka da yin hakan Ce-ce-ku-ce yayi kamari, har takai Joshua ya kulle Charity a É—aki sannan ya yi mata dukan da yasa ta mutu.
  • Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Joshua Ukandu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa za a gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here