Rashin albashi yasa ma’aikatan gwamnatin tarayya yin kirsimeti babu armashi

0
29

Ma’aikatan gwamnatin tarayya mabiya addinin kirista sun gudanar da bikin kirsimeti cikin yanayi mara armashi sakamakon jinkirin da aka samu wajen biyan su albashin watan Disamba.

Jaridar Punch, ta rawaito cewa ma’aikatan sun fuskanci matsalar samun albashin watan Nuwamba a kan lokaci, wanda bincike ya bayyana cewa mafi yawancin ma’aikatan gwamnatin tarayya basu samu albashin watan Nuwamba ba, sai a farkon Disamba.

Wasu majiyoyi sunce ana samun matsalar tsaikon biyan albashin daga babban akanta na kasa, a daidai lokacin da wasu ke cewa sauya manhajar biyan albashin da akayi ne ya kawo tsaikon.

Punch, tace ma’aikatan gwamnatin tarayya sun bayyana bacin ran su akan rashin albashin lokacin da ake zantawa dasu a ranar talata.

A wasu lokutan akan samu gwamnatin tarayya zuwa ta jihohi su biya albashi akan lokaci in bikin kirsimeti ya gabato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here