Dakarun Sojin Nigeria na hadin gwiwa sun yi karin haske akan harin da suka kai wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa a ƙaramar hukumar Silame ta jihar Sokoto.
Sojojin sun kai harin a jiya Laraba, da aka tabbatar yayi ajalin fararen hula kusan 10, a kauyuka.
A wata sanarwa da kakakin sojin, Laftanar kanal Abubakar Abdullahi, ya fitar, kan zargin sojoji da kai wa fararen hula hari, ya ce sun kai hare-haren ne bayan samun bayanan sirri akan yan ta’adda irin su Lakurawa, saboda dole a tabbatar harin ya kai gare su.
Sojin Nigeria sun kara da cewa ba fararen hula suka kaiwa hari ba, sun kai farmakin ne kan yan ta’adda.
Sun kuma nemi al’umma su rika tantance bayanan da ake yadawa don kaucewa yada labaran karya.
Sanarwar ta kara da cewa, yankunan Gidan Sama da Rumtuwa da aka kai hare-haren, yankuna ne da aka gano akwai yan ta’addan Lakurawa a wajen.