Wani bincike da manyan kafofin yada labarai suka gudanar ya tabbatar da cewa babu gaskiya a zancen kai harin kunar bakin wake zuwa babban bankin kasa CBN dake birnin tarayya Abuja a jiya alhamis.
Wasu daga cikin masu amfani da kafafen sada zumunta, musamman yan arewa ne suka rika yada jita jitar kai harin tare da nuna wani hoton da ake cewa CBN ne aka yi masa mummunar barna da bama-bamai.
Amman binciken ya nuna cewa hotunan da aka yada ba gaskiya bane, sun kasance wadanda aka samar da kirkirarriyar basira wato AI.
Masu yada labarin sun yi ikirarin cewa an tafka asarar da takai Dala biliyan 100, a sanadiyyar harin.
Kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani akan gaskiyar kai harin, saboda babu wani daga cikin sashin tsaron Nigeria daya gasgata batun.
Akan haka ne ake neman al’umma suyi watsi da jita jitar.