Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya nemi shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya dakatar da shirin da yake yi a fannin tattara kudaden harajin da yake nufin aiwatarwa.
Bala Muhammad, ya nemi hakan a jiya Alhamis lokacin, daya shiryawa kiristoci bikin Kirsimeti a jihar.
Ya ce ƙudurorin ba za su yi wa ƴan arewa kyau ba, inda ya ce gwamnoni ba za su iya biyan albashi ba in har aka samar da dokar.
A cewar Bala Muhammad, dole a saurari bukatar yan Arewa, yana mai cewa kin yin hakan zai zama kama karya.
Kamar yanda sauran al’ummar arewa suke fada, gwamnan yace an tsara yin gyaran dokar harajin don cin ribar jihar Legas kadai, wanda yace kamata yayi a samar da dokar da zata hada kan al’umma ba janyo kabilanci ba.