Rundunar sojin Nigeria ta ce bama-baman da Lakurawa suka ajiye a ƙauyukan da sojojin suka kai wa hari ne suka kashe mutanen gari, ba hare-haren da sojojin suka ƙaddamar ba.
Akalla mutane 10 ake zargin harin sojojin Nigeria ya hallaka a ranar larabar data gabata, lokacin da suka kaiwa Lakurawa hari a yankin ƙaramar hukumar Silame a jihar Sokoto.
Sai dai gwamnan jihar, Ahmad Aliyu, ya ce sojojin ne suka kai harin bisa kuskure, sannan ya nemi al’umma su dauki hakan a matsayin kaddara.
Bayan samun cece-kuce akan harin shalkwatar tsaron ƙasa ta fitar da wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaran ta, Manjo Janar Edwar Buba, ya ce ba harin sojojin ne ya kashe mutanen ba, bama bamai ne da Lakurawa suka ɗana.
Ya ce kafin kai harin, sai da sojojin suka ɗauki tsawon lokaci suna gudanar da cikakken bincike ta hanyar tattara bayanan sirri, sanna suka tabbatar da cewa Lakurawa ne ke cin karen su babu babbaka a yankin.
Wannan dai ba shine karon farko da ake samun kashe fararen hula ba, daga bangaren sojoji wanda sojin ke cewa hakan na faruwa bisa kuskure.