Wike ya musanta zargin da akayi masa na kwacewa mutane filaye a Abuja

0
34

Ministan Abuja Nyesom Wike, ya musanta zargin da akayi masa na cewa yana kwacewa mutane filaye a birnin tarayya Abuja, inda ya bayyana cewa shi ya kasance mai yakar duk masu halayyar kwacewa mutane filaye.

Ministan ya sanar da hakan a ranar Alhamis a wajen wani taron da ƴan PDP na ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas ta jihar Ribers, suka gudanar inda ya yi godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bisa damar da ya ba shi, a cikin gwamnatin sa har ya zama minista.

A cewar Wike, bazai kwace fili ba, tunda shine yake da iko akan kowanne filin birnin.

Ya ƙara da cewa yanzu ba kamar Rivers ba, da ƴan Najeriya baki ɗaya yake aiki, wanda hakan ya sa shi ya ƙara fahimtar wasu abubuwa.

A kalaman nasa yayi nuni da cewa gwamnatin baya bata bi ka’ida ba wajen kula da lamarin filaye yana mai cewa a yanzu shi zai taka burki ga duk wani kalubalen da fannin filaye ke fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here