Kamfanin rarraba lantarki na Nigeria TCN ya sanar da mazauna birnin tarayya Abuja, cewa za’a fuskanci daukewar wutar lantarki a wasu sassan birnin.
Mai magana da yawun kamfanin Ndidi Mbah, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa data fitar a yau asabar, tana mai cewa injiniyoyin TCN zasu yi gyaran lantarki na tsawon ranakun asabar da lahadi.
Tace za’a yi aikin a wani injin lantarki mai karfin 60MVA dake karkashin karamar tashar lantarki ta Gwagwalada, mai karfin lantarki 330/132/33kV.
Sanarwar tace kamfanin rarraba lantarki na Abuja, ba zai bayar da lantarki ba, a tsawon Lokacin da ake yin gyaran.