Gwamnatin zata fara biyan mafi karancin albashi na naira dubu 70

0
46

Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikatan ta.

Mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa daga yanzu gwamnatin jihar zata fara biyan mafi karancin albashin naira dubu 70, ga daukacin ma’aikata.

Ya kara da cewa gwamnan jihar Dauda Lawal, ya amince zai bayar da alawus na wata É—aya ga ma’aikata jihar.

Sanarwar tace wannan kokari da gwamnan yayi shi ne irinsa na farko a tarihin Zamfara.Sulaiman ya ce dukkan ma’aikatan jihar, ciki har da waÉ—anda suka yi ritaya za su samu kashi 30 na alawus.

Gwamnan Dauda Lawal ya ce ya amince da albashi mafi Æ™anÆ™antan da kuma alawus ne domin taimakawa ma’aikatan jihar a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara da kuma Æ™ara musu karfin gwiwa wajen aiki tukuru wajen kai jihar gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here