Gwamnatin tarayyar Nigeria ta samu damar karbar bashin bankin duniya daya kai dala biliyan 1 da rabi, bayan cika sharadin cire tallafin fetur da sauran tsare tsaren da suka shafi fannin kudi.
Bisa yarjejeniyar da gwamnatin tayi da bankin duniya zai bata dala biliyan 1.5, na gyaran tattalin arziki sai kuma dala miliyan 750, na ayyukan cigaban al’umma.
Daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin ta aiwatar akwai cire tallafin man fetur, da kuma bijiro da sabuwar dokar gyaran haraji da ke gaban majalisar dokoki.
An raba bashin ne gida biyu zuwa miliyan 750 kowanne, inda tun ranar 2 ga watan Yulin 2024 aka bai wa gwamnatin Najeriya kason farko, kamar yadda wani ƙunshin takardu da bankin ya fitar ya nuna.
Amma kuma sai a watan Nuwamba aka ba ta kaso na biyun saboda sharuÉ—É—an bayar da shi na tattare da aiwatar da tsare-tsaren tattalin arzikin da gwamnatin ta Bola Tinubu ke yi a yanzu.
Sai dai a kwanakin baya asusun bayar da lamuni na duniya, yace bashi da hannu wajen cire tallafin fetur da Nigeria tayi, wanda ake ganin yawan cin bashin da gwamnatocin kasar keyi na daga cikin dalilan fadawar talaka cikin kuncin rayuwa.