Lauyan Bello Bodejo, Reuben O. Atabo SAN ne ya gabatar da bukatar neman belin Bodejo, wanda yace ana tsare Da shi tun ranar 9 ga watan Disamba 2024 ba tare da an gabatar da shi a gaban kotu ba.
A zaman ta na biyu a ranar Litinin, Babbar kotun tarraya karkashin mai Shari’a Muhammad Zubair ta bayar da belin Bello Bodejo tare da sharadin duk lokacin da aka bukaci Bodejo, Lauyan shi zai gabatar da shi.
Daga karshe Alkalin kotun ya bayyana tsare Bodejo da aka yi, ya sabawa doka.
Jami’an tsaron farin kaya DSS, ne suka kama shi bisa zargin sa da kafa kungiyar tsaro ta sa-kai ba bisa ka’ida ba.