Majalisar dattawa ta Nigeria ta sanar da yan kasar cewa kasafin kudin shekarar 2025 ba zai fara aiki da zarar an shiga sabuwar shekara ba.
A bisa ka’ida za’a fara amfani da kasafin kudin a ranar 1 ga watan shekarar 2025, bisa hujjar karewar wa’adin yin amfani da kasafin kudin shekarar 2024.
:::Kamfanin NNPCL yace an gyara matatar fetur ta Warri
A ranar 18 ga watan Disamba ne shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya gabatarwa da yan majalisun dokokin kasar kasafin naira tiriliyan 49.7.
Shugaban kwamatin yaÉ—a labarai na majalisar, Sanata Yemi Adaramodu, ya sanar da cewa sai a ranar 7 ga watan Janairun 20235 za su fara sauraron jawabin kare kasafi na hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya.
Ya ƙara da cewa kwamatin kula da harkokin kuɗi na majalisun zai gabatar da rahotonsa na ƙarshe a ranar 31 ga watan na Janairu.
Idan za’a iya tunawa a yayin da Tinubu, ya gabatarwa da majalisar kasafin, shugaban Majalisar dattawa Akpabio, yace sun tsawaita wa’adin yin amfani da kasafin 2024, zuwa tsakiyar shekarar 2025.