Nan da makonni masu zuwa ake kyautata zaton shugaban Nigeria Bola Tinubu, zai sanar da sunayen mutanen da zai nada a matsayin jakadun kasar a kasashen waje.
:::http://Ya kamata a biya diyya ga wadanda sojoji suka kashe a Sokoto—PDP
Babban mai taimakawa shugaban a fannin harkokin kasashen ketare da tsare-tsare, Ademola Oshodi, ne ya sanar da hakan ranar lahadi, lokacin da yake zayyano abubuwan da suka gudanar a shekaar 2024, yayin wata zantawa da tashar talbijin ta Channels.
Oshodi, yace yana da imanin nan da wasu makonni masu zuwa za’a bayyana sunayen wadanda zasu wakilci Nigeria a huldar diflomasiyyar ketare, da kuma mika sunayen su ga majalisa don tantancewa da kuma bayyanawa kowa kasar da za’a tura shi.
Idan za’a iya tunawa a ranar 2 ga watan Satumba na shekarar 2023, ne shugaban kasar ya yiwa daukacin jakadun Nigeria Kiranye, kuma har kawo wannan lokaci ba’a nada wasu jakadun ba.