Rundunar Hisbah ta jihar Kano, ta jaddada cewa har yanzu akwai dokar data hana cigaba da gudanar da bukukuwa ko taruwar maza da mata a guraren taruwar al’umma don gudanar da wani sha’ani wanda aka fi sani da (Event Center).
Babban kwamandan rundunar Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya sanar da hakan ta bakin mataimakin sa, Dr Mujahiddin Aminudden Abubakar.
Tun a kwanakin baya, Hisbah, ta bayyana cewa dadewar da akeyi lokacin gudanar da bukukuwa zuwa tsakar dare na taka rawa wajen lalata tarbiyyar matasa maza da mata, da wani lokacin maza ke yin amfani da hakan don aiwatar da mummunan nufi ga wasu matan.
Haka zalika wasu matan na fakewa da dadewar da akeyi a gurin bikin don tafiya yawo inda bai dace ba.
Wadannan dalilai na daga cikin hujjar jaddada dokar tashi daga guraren biki da zarar karfe 11 na dare, tayi a jihar Kano, bayan korafi da al’umma ke kaiwa Hisbah dangane da lalacewar tarbiyyar matasa a wajen biki.
Rundunar Hisbah tace ta gudanar da wani taro tare da masu guraren biki event center, inda aka samar da dokokin kiyaye tarbiyyar al’umma, da suka kunshi, hana cakuduwar maza da mata, hana saka wakokin batsa, sai hana cikawa mutane kunne da karar wakokin, tare da umartar mutane su rika yin Sallah duk lokacin Sallar farilla, hana yin rawar banza.
Hisbah ta kara da cewa zata dauki matakin shari’a akan duk wanda ya karya wadannan dokokin daga farkon shekara mai kamawa ta 2025.
A wani cigaban kuwa, Hisbah ta samu nasarar kama wani mutum da yake aikin bokanci, a unguwar Sheka, dan shekara 50, mai suna Umar.
Al’ummar unguwar ne suka kaiwa Hisbah, korafi akan bisa zargin sa da kawalci, da tsibbu, inda aka same shi tare da namiji daya da mace daya.
Hisbah, ta sanar da cewa za’a gudanar da bincike akan sa don daukar matakan da suka dace.