Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya saka hannu akan kasafin kudin shekarar 2025, da yawan sa yakai naira biliyan 719.
Kasafin wanda aka yiwa lakabi da kasafin kyautata fata ga ayyukan cigaba da kuma cigaban tattalin arziki, ya kunshi naira biliyan 457 na manyan ayyuka sai biliyan 262, na ayyukan yau da kullum.
Abba Kabir, yace kasafin zai taimakawa cigaban jihar Kano, har zuwa Shekaru masu yawa da zasu zo nan gaba.
Abba, ya sanya hannu akan kasafin ne bayan da kakakin majalisar dokokin jihar Ismail Falgore, ya gabatar da shi ga Gwamnan a yau Talata.