Gwamnan Rivers ya gabatar da kasafin jihar ga yan majalisa 3

0
36

Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya gabatar da kasafin kudin jihar da yawan sa yakai naira triliyan 1.18, ga yan majalisar dokokin jihar, masu goyon bayan sa su uku kacal, a ranar litinin data gabata.

:::Muna so Kwankwaso ya dawo cikin mu kafin shekarar 2027—PDP

Haka ya kasance makamancin abun da Fubara, ya aikata a shekarar data gabata inda yaki gabatar da kasafin ga yan majalisar dake goyon bayan tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike, su 27, tare da gabatar da kasafin ga zallar yan majalisar dake yi masa biyayya.

Fubara, ya kasance yaron Wike, a siyasance wanda shine ya zama silar hawansa mulkin Rivers, sai dai dangantaka tayi tsami a tsakanin su, musamman akan karfin fada aji a harkokin gwamnatin Jihar, haka ne yasa kan yan majalisar jihar Rivers, ya rabu biyu inda mafi yawan yan majalisar ke goyon bayan Wike, da bijirewa umarnin Fubara.

Wannan gabatar da kasafi da Siminalayi Fubara, yayi a jiya ya sanya wasu daga cikin yan jam’iyyar adawa ta APC, bayyana cewa gwamnan yana kokarin aikata abun da yaci karo da doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here