Tinubu ne mutum na uku cikin wadanda suka fi aikata cin hanci a shekarar 2024–OCCRP

0
86

Shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya samu matsayi na uku a jerin Sunan mutanen da suka yi kaurin suna wajen aikata laifin cin hanci da rashawa, da kuntatawa al’umma a shekarar 2024.

Kungiyar, binciken laifuka da cin hanci, ta (OCCRP) ce ta sanar da jerin sunayen manyan mutanen masu karfin cin hanci a shekarar 2024.

Shugaban Kenya, William Ruto, ne yazo na daya, sai tsohon shugaban kasar Indonesia Joko Widodo, sannan Tinubu, yazo na uku.

OCCRP ta bayyana wadannan matsayin na cin hanci, ta hanyar karɓar ƙuri’u daga mutane daban-daban a duniya, don gano wadanda suka taka rawa sosai wajen haɓaka cin hanci, rashin gaskiya, da ƙara talauci a ƙasashen su.

A bangare guda tsohon shugaban kasar Syria, Bashar Al Assad, ne ya samu matsayin wanda yafi dadewa yana kwashe dukiyar kasar sa, wanda ya gudu zuwa Turkiyya, bayan kifar da Gwamnatin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here