Bamu da shirin mayar da kananun hukumomi karkashin gwamnatin tarayya—Tinubu

0
48

Shugaban Nigeria Tinubu, ya musanta zargin da akayi na cewa yana yin takun saka da gwamnonin kasar akan dokar bawa kananun hukumomi cin gashin kansu.

Idan za’a iya tunawa a watan Yulin shekara ta 2024, ne kotun koli ta zartar da hukuncin bawa kananun hukumomin kasar nan 774, yancin kai dangane da al’amuran kudaden su.

Haka ne yasa mafi yawancin Gwamnoni suka gudanar da zabukan kananun hukumomi don gujewa abinda kaje yazo na yiwuwar kin basu kason kananun hukumomi na kudi daga asusun gwamnatin tarayya.

Sai dai a lokacin da gwamnonin kasar nan baki daya suka gana da Tinubu, don taya shi murnar shiga sabuwar shekara, yace musu tabbas suna da rawar takawa wajen cigaban kasa, tattalin arziki, noma da sauran su.

Haka zalika Tinubu, ya nemi hadin kan gwamnonin don hada kai da gwamnatin tarayya ta fuskar ciyar da kasa gaba, da magance kalubalen da kasar ke ciki musamman dangane da batun yancin kananun hukumomi, inganta harkokin noma, da daga darajar naira.

A nasa jawabin Shugaban kungiyar gwamnonin kasar nan, Abdulrahman Abdulrazak, yace manufofin da ake aiwatarwa na inganta harkokin noma, suna haifar da sakamako mai kyau, a fadin Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here