Bokayen Jamhuriyar Nijar, sun dauki aniyar yin amfani da gungun aljanu akan Ƙasashen dake yiwa kasar su zagon kasa.
Hakan ya biyo bayan yadda Shugaban mulkin sojin Nijar, janar Abdoulrahamane Tciani, ya gana da wasu kungiyoyin Bokayen Nijar da na wasu kasashen Afrika.
A yayin ganawar ta su kungiyoyin Bokayen sun yi alkawari ga shugaban kasar cewa za suyi amfani da gungun aljanu wajen afkawa duk wasu kasashe da ke yi wa Nijar din zagon kasa.