Gwamna Nassarawa, Abdullahi Sule ya sauke ɗaukacin kwamishinonin sa tare da Sakataren Gwamnatin Jihar.
Bayan haka gwamnan ya sauke dukkanin masu bashi shawara.
Gwamna, Sule, ne ya bayyana hakan ne a wani taron gaggawa daya gudanar a gidan gwamnatin jihar Nassarawa dake Lafia a yau Juma’a.
Ya sanar da daukar matakin korar yan majalisar zartarwar tasa ne jim kadan bayan tafiyar mataimakin shugaban kasa Kashim Shetima wanda ya kai ziyarar aiki ta kwana daya a jihar domin kaddamar da wasu ayyuka a jihar.
Kawo yanzu dai ba’a bayyana cikakken dalilin dauke masu rike da mukaman ba.