Gwamnan Abba Kabir Yusuf ta amince da rage kudin rijistar dalibai na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil.
Daga yanzu yan asalin Jihar Kano za su rika biyan kudin rijistar dalibai wato registration fee, Naira 23,000, sabanin naira 43,000 da suke biya a baya, wanda Gwamnati za ta biya kashi 50% kuma dalibai za su biya sauran kashi 50%.
Sai kuma wadanda ba ‘yan asalin Jihar ba za su biya N115,000 maimakon N163,000, da suke biya a baya.