Gwamnan Borno zai mayar da farashin litar fetur naira 600 ga manoma

0
20

Gwamnan jihar Borno, ya sanar da cewa gwamnatin sa zata samar da tallafin man fetur ga manoman yankunan da suka fuskanci matsalar rashin tsaron Boko Haram.

Zulum, ya sanar da hakan a jiya juma’a lokacin da yaje kaddamar da rabon tallafin kayan aikin noma ga manoma fiye da dubu biyar wanda rikicin Boko Haram, ya raba su da muhallin su, a karamar hukumar Bama.

Gwamna Zulum, yace a yanzu zai mayar da farashin kowacce Lita naira 600, sabanin naira 1000, zuwa 1200, da ake siyarwa.

Gwamnatin Borno, tace wannan manufa tana tattare da niyyar kakkabewa manoma matsalar karancin kudin da suke fuskanta saboda matsalolin tsaro.

Zulum, yace irin wannan mataki da aka dauka a kananun hukumomin Mobar, da Damasak, yasa an samu habbakar amfanin gona.

Zulum, ya kara tabbatar da cewa za’a fara siyar da litar man fetur akan farashin naira 600, ga manoman da zarar lokacin noman rani ya fara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here