An kama matashin da yayi garkuwa da yaro dan shekara 2 a Kano

0
36

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama wani matashi mai shekaru 25, kan zargin sace wani yaro ɗan shekara biyu mai suna Al’amin Ahmad Garba, tare da neman kuɗin fansa Naira miliyan 50.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 25 ga watan Disamban 2024.

An samu yaron a wani gida dake unguwar Dorayi, bayan ya kwashe kwanaki uku ba’a san inda yake ba.

Bayan an ceto yaron, an kai shi Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad don duba lafiyarsa, sannan aka miƙa shi ga iyayensa.

An gurfanar da wanda ake zargin a kotun majistare mai lamba 25 da ke Nomansland, a Kano.

Zuwa yanzu matashin yana tsare a hannun hukuma, yayin da ake ci gaba da shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here