Kungiyar dattawan arewa ta (NEF) ta sake nuna damuwa akan kudirin dokar harajin Tinubu, inda ta nemi a gaggauta Janye aniyar samar da dokar, tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki akan yanda ya kamata a bullowa batun sauya fasalin dokar harajin.
Kungiyar ta kalubalanci gwamnatin tarayya, akan yadda ta kirkiro dokar harajin ba tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki ba.
Kungiyar ta NEF, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa data fitar a jiya asabar mai dauke da sanya hannun jagoran ta Amin Daggash, yana mai cewa tabbas dokar harajin zata kawo nakasu ga arewa da kasa baki daya.
Daggash, ya kara da cewa yan arewa da al’ummar Nigeria basa kalubalantar samar da wata doka in har zata zama mai amfani daga matakin kasa zuwa kananun hukumomi.