Gwamnatin Kano ta sanar da ranakun komawa makarantun boko

0
48
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana ranakun 5 da 6 ga watan Janairu, 2025 a matsayin ranakun da ɗalibai za su koma makarantu, domin fara zangon karatu na biyu na shekarar 2024/2025.

Gwamnatin, ta bayyana cewa dukkanin makarantun kwana, na gwamnati da masu zaman kansu, za su koma a yau Lahadi, 5 ga Janairu, 2025.

Makarantun jeka-ka-dawo kuma za su fara komawa ranar Litinin, 6 ga Janairu, 2025.

Bayanin hakan ya fito cikin wata sanarwa da Balarabe Abdullahi Kiru, Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi, ya fitar.

Sanarwar tayi kira ga iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma a kan lokaci.

Sanarwar ta gargaɗi cewa ɗaliban da suka kasa komawa a kan lokaci za su fuskanci hukunci.

Sannan za a sa ido domin tabbatar da cewa malamai da ma’aikata suna aiki yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here