Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, ta kama wata mata mai suna Khadija Ali, bisa zargin ta da jefar da yaron data haifa bayan kwana daya saboda kuncin rayuwa da take ciki.
Kakakin rundunar yan sandan Abuja SP Josephine Adeh, ce ta sanar da hakan a yau lahadi, cikin wata sanarwa data fitar.
Sanarwar tace an samu jaririn da aka jefar mai kimanin kwana daya a duniya a ranar juma’a data gabata bayan an kaiwa yan sanda rahoton samun ajiye yaron.
A cewar ta, jaririn, wanda aka nade shi da wani zani, an ceto shi tare da kai shi cibiyar kula da lafiya a matakin farko dake yankin Mpape don a duba lafiyarsa.
Ta kara da cewa, bayan gwaje gwajen da aka yi masa, sun tabbatar da cewa jaririn yana cikin koshin lafiya.
Rundunar yan sandan tace ta samu bayanan sirri daga al’ummar yankin, tare kama mahaifiyar jaririn, Khadija Ali, inda ta bayyana cewa ta jefar da jaririn ne saboda rashin ikon kula da shi saboda talauci bayan mijin ta ya gudu.
Sanarwar tace za a gurfanar da matar a gaban kotu bisa zargin karya dokar Kare hakkin yara, sashe na 14 da 16, ta shekarar 2003.