Mutane 9 ne suka mutu biyo bayan wani rikicin da ake kyautata zaton cewa na kabilanci ne a kauyukan Gululu da ‘yan Kunama, dake jihar Jigawa.
Wasu matasan Fulani da ake zaton sun bude shagon adana kayan masarufi sannan suka sace su, sune suka haddasa faruwar rikicin.
Sai dai zuwa yanzu, an samu nasarar shawo kan rikicin wanda kuma ya janyo asarar gidaje da dama.
Mai magana da yawun rundunar Æ´an sandan Jigawa, DSP Lawan Shi’su Adam, ya shaida wa BBC cewa an tura jami’an tsaro zuwa inda abun ya faru karkashin jagorancin kwamishinan Æ´an sandan jihar zuwa yankin domin kwantar da hankalin al’umma, inda yace za’a gudanar da bincike akan masu laifi da kuma hukunta su.
Ya ce hankali ya fara kwanciya a garuruwan kuma jami’an tsaro suna ta kai kawo don tabbatar da cewa ba a sake samun tashin hankali ba.