Gwamnan Kano ya rantsar da sabbin kwamishinoni 7

0
34

A yau Litinin ne Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da sabbin kwamishinoni 7 da ya nada bayan majalisar dokokin jihar, ta tantance tare da amincewa da su.

Cikin kwamishinonin akwai tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnan, Shehu Wada Sagagi.
Gwamna Abba,ya kasance a tare da kwamishinonin yayin da ake basu rantsuwar kama aiki.

Kwamishinan shari’a na Kano Kuma babban lauyan jihar, Barista Haruna Isa Dederi shine ya rantsar da sabbin kwamishinonin 7 tare da sauran masu baiwa gwamna shawara.

Sabbin Kwamishinonin da gwamna Yusuf ya jagoranci rantsarwa sun hada da;

1.Alhaji Shehu Wada Sagagi, da zai kula da ma’aikatar kasuwanci da zuba jari ta kano

2.Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya, zai kula da ma’aikatar yada Labarai.

3.Dr.Dahir Muhammad Hashim, ma’aikatar Muhalli.

4.Abdulkadir Abdussalam, ma’aikatar Raya karkara.

5.Dr. Isma’ila Aliyu Dan Maraya ma’aikatar Kudi.

6.Dr.Gaddafi Sani Yakubu, ma’aikatar makamashi.

7.Dr.Nura Iro Ma’aji , ma’aikatar Kula da kwangiloli da bibiyar ayyukan gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here