Kungiyar SERAP, mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa, da tabbatar da shugabanci na gari, ta nemi shugaban kamfanin mai na NNPCL Mele Kyari, ya yi bayani game da zargin bacewar sama da Naira biliyan 825 na kudin shigar mai da kuma dala biyan biyu da miliyan ɗari biyar da aka ware domin gyaran matatun man kasar nan.
Bukatar hakan ta biyo bayan rahoton shekarar 2021 da babban mai binciken kudi na gwamnatin tarayya ya gabatar, wanda ya nuna damuwa akan yadda ake tafiyar da kudaden gwamnati a hukumar NNPC.
Wani binciken da SERAP ta yi a kwanan nan, da aka fitar a ranar 27 ga Nuwamba, 2024, ya nuna yadda alkaluman wasu kudade suka ci karo da juna, ciki har da kudaden da ba’a san abin da aka yi da su ba.
Kudin ya kunshi naira biliyan 825 da ake zargin an cire na kudin danyen man da aka sayar, da kuma dala biliyan biyu da miliyan dari biyar na gyaran matatun man Nigeria tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021.
Ofishin babban mai binciken kudin ya nuna cewa mai yiwuwa an karkatar da kudaden wanda ya bukaci a gudanar da cikakken bincike tare da nemo kudaden.
A cewar Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, dole ne a mika wadanda ke da hannu wajen karkatar da kudaden ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da hukumar ICPC, don yin adalci ga yan kasa akan dukiyar da ake sace musu