Dakarun Sojin Nigeria na rundunar hadin gwiwa ta 1, dake atisayen Fansan Yamma, a yankin arewa maso yamma sun yi nasarar kashe wani fitaccen dan ta’adda mai suna Sani Russu a Zamfara.
Hakazalika sojojin sun samu nasarar kai hare-hare daban-daban kan ‘yan ta’adda a jihar tare da kwato makamai.
Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa, da shugaban sashin yada labarai na rundunar Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi, ya fitar yau litinin a Gusau.
Sanarwar tace a ranar 4 ga watan Janairu, sojojin sun gudanar da sintiri zuwa kauyen Bamamu da ke karamar hukumar Tsafe a Zamfara inda suka yi arangama da ‘yan ta’adda a yankin, wanda haka ne yasa suka kashe Sani Rusu.
A wancan lokaci Sojojin sun kai wani harin kwanton bauna bayan samun bayanan sirri game da ayyukan ta’addanci a Kwanar Jollof da ke karamar hukumar Shinkafi, Kuma sojojin sun kashe wasu ‘yan ta’addan yayin da wasu suka samu munanan raunuka.
Ya kuma kara da cewa, an samu nasarar kwato bindiga kirar AK47 guda daya da kuma bindigar G3 guda daya, tare da harsashai na musamman guda takwas na 7.62mm, harsashai na NATO har guda hudu 7.62mm, da babura uku.
A wani samame na daban, rundunar sojin sama ta atisayen Fansan Yamma ta kai farmaki ta sama kan ‘yan ta’addan da suke haduwa a tsakanin Fakai da yankin Kware a Shinkafii a ranar 30 ga watan Disamba.
An kaddamar da wannan hari ta sama a matsayin martani ga bayanan sirri da ke nuni da cewa ‘yan ta’adda karkashin jagorancin Bello Turji sun gudanar da taro a yankin.
A wani samame da rundunar ta kai a ranar 2 ga watan Janairu, Rundunar Sojan Sama ta kara kai hari a yankin Maikaman Rini da ke dajin Sububu tare da goyon bayan masu atisayen Fansan Yamma da sojojin kasa da ke yaki da ‘yan ta’adda a sansanin Ibrahim Chumo.