Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kori ma’aikatan ta su 27 saboda aikata laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa ko kuma almundahana.
EFCC tace aikata wadannan laifuka sun sabawa ka’ida da dokokin ta, don haka dole ne a dauki matakin hukunta masu laifin.
Sai dai hukumar bata bayyana suna ko muƙaman jami’an da ta kora ba, amma ta bayyana cewa shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ne ya amince a kori masu almundahanar.
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya ce an kori ma’aikatan da abin ya shafa bayan karɓar rahoton kwamitin bincike da ladabtrwar hukumar da ta binciki zarge-zargen da ake musu, kuma aka same su da laifi.
Ya Æ™ara da cewa hukumar za ta binciki zargin almundahanar Dala dubu É—ari huÉ—u da ake yiwa wani jami’in ta da zargin ke yawo a kafofin sada zumunta.