An rantsar da John Mahama, a matsayin sabon shugaban kasar Ghana, a karo na biyu.
Mahama ya taɓa mulkar Ghana a matsayin shugaban kasar a tsakanin shekarun 2012 zuwa 2017.
An rantsar da John Mahama ne a dandalin Black Star da ke Accra babban birnin kasar.
An kuma rantsar da Naana Jane Opoku-Agyemang, a matsayin mataimakiyar shugabar kasa, wadda ta zama mataimakiya mace ta farko a kasar.
Taron rantsuwar ya samu halartar manyan mutane daga sannan duniya.