Gwamna Katsina ya yiwa majalisar zartarwar sa Garanbawul

0
43

Gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Radda, yayi garambawul ga majalisar zartarwar sa, inda ya sauyawa wasu kwamishinoni ma’aikatu.

Daga cikin wadanda aka sauyawa ma’aikatun akwai Yusuf Rabi’u Jidede, wanda ya koma kwamishinan ma’aikatar ciniki wanda a baya yake a matsayin kwamishinan ayyuka na musamman.

Sai Adnan Na’habu daga ma’aikatar ciniki zuwa ta ayyukan musamman.

A dan wannan lokacin nan gwamnoni da dama sun gudanar da garambawul ga majalisun zartarwar su, inda suke bayyana cewa suna yin haka ne da manufar inganta harkokin gudanar da gwamnatin.

A wani sa’in ana korar kwamishinonin wani lokacin kuwa a sauyawa wasu ma’aikatu.

Ko a yau Talata, sai dai aka samu yin garambawul daga gwamnatin jihar Bauchi, inda gwamnan jihar Bala Muhammad, ya kori kwamishinonin sa biyar, da kuma zabo mutane 8, zai basu wasu mukaman.

Ko a kwanakin baya shima gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya kori kwamishinonin sa biyar, tare da rantsar da sabbin kwamishinoni 7 a jiya litinin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here