Gwamnatin tarayya ta himmatu wajen yin bincike a manyan filayen jiragen sama domin hana yaɗuwar cutar HMPV mai kamanceceniya da coronavirus da ta ɓulla a ƙasar China.
Ministan lafiya Muhammad Ali Pate, ya umarci ma’aikatan lafiya da ke filayen jirage su fara gwada fasinjojin da ke shigowa ƙasar nan domin gano masu ɗauke da cutar, inda jaridar Daily trust, ta ce an fara gwajin matafiya a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas da na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
A lokacin da cutar Covid-19 ta ɓulla a shekarar 2020, wani fasinja mai shekara 44 ɗan asalin ƙasar Italiya ne ya shigar da cutar Najeriya ta filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a ranar 24 ga Fabrairun 2020.
Cutar ta HMPV, wadda ta fara ɓulla a China, yanzu ta fara yaɗuwa a India da Malaysia da Kazakhstan, sannan aƙalla mutum 5,000 ne ake tunanin cutar ta kwantar a Birtaniya.