A kwanakin baya ne dai Kotun ɗaukaka ƙara a jihar Kano ta sassauta hukuncin ɗaurin shekara 24 da aka yanke wa Mubarak Bala bisa laifin ɓatanci ga addinin Musulunci zuwa shekara biyar.
A cewar lauyan Mubarak mai suna James Ibori, kotun ta ce hukuncin kotun na farko ya yi tsauri kuma ya saɓa wa doka.
Tun a shekarar 2020 aka kama Mubarak Bala, bisa zargin yin ɓatanci ga addini a shafinsa na Facebook.
Sai a 2022 aka ɗaure shi shekara 24 bayan ya amsa laifukan da ake tuhumar sa da aikatawa.