Peter Obi da iyalan sa na fuskantar barazana da rayuwar su

0
39

Dan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar LP a kakar zabe ta 2023, Peter Obi, ya ce, yana fuskantar barazana da rayuwar sa, saboda yana kalubalantar manufofin gwamnatiin Tinubu.

Yace barazanar ta fito fili tun bayan da ya fitar da sakon sa na shiga sabuwar shekarar 2025.

A saƙon nasa na sabuwar shekarar, Obi ya bayyana cewa Najeriya na fama da taɓarɓarewar tattalin arziki da rashin tsaro da rashin ingantaccen kiwon lafiya.

Obi yayi tambayar cewa shin abun daya fada ya sabawa ka’ida ko wuce iyaka ne.

Dan takarar ya sanar da hakan a sakon daya wallafa a shafin sa na X, yana mai cewa ana yiwa rayuwar sa da iyalin sa barazana, sannan yace wani mai suna Felix Morka ya zarge shi da wuce iyaka, sannan ya yi barazanar cewa Obi zai ɗanɗana kuɗar sa akan bayyana ra’ayin sa da yayi akan yadda al’amura ke gudana a Nigeria.

Obi ya ƙara da cewa idan har da gaske ya karya doka, a nuna wajen da yaci karo da ka’ida a kalaman sa, inda ya ƙara da cewa, ba zai daina faɗin gaskiya ba, musamman a wannan lokacin da Nigeria ke fuskantar matsalolin shugabanci da tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here