Tsohon DPO na Bompai Daniel Amah ya karbi addinin muslinci

0
51

Wani fitaccen ɗan sanda mai muƙamin ACP, Daniel Amah ya karɓi addinin Musulunci.

Zuwa yanzu Amah, ya sauya suna zuwa Muhammad Sunusi, da aka bayyana cewa ya jima yana yin abubuwan alkairi ga addinin muslinci.

Majiyar, Nasir Salis Zango, dake aiki a kafar yada labarai ta Freedom Radio dake Kano, tace a baya Muhammad Sunusi, (Amah) har gina masallaci yayi lokacin da yake shugabantar ofishin yan sandan Bompai.

Bisa yadda al’umma ke bayyana Muhammad Sunusi, yayi fice wajen aikata duk abubuwan da addinin muslinci ya kwadaitar.

Idan za’a iya tunawa ko a baya ASP Daniel Amah, wato Muhammad Sunusi, a yanzu, ya taba kin karbar cin hanci na dalar Amurka $200,000 kwatankwacin naira miliyan 83.87, a wancan lokacin, adomin toshe wani laifi na fashi da makami.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here