Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da shirin da take yi na dasa bishiyu miliyan 10 a fadin jihar don yaki da dumamar yanayin da duniya ke fama da shi.
Kwamishinan muhalli na Kaduna, Abubakar Buba, ne ya sanar da hakan a yau laraba lokacin, gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki a jihar, yana mai cewa manufar hakan itace a rage kaifin illar dake tattare da dumamar yanayi da kiyaye muhalli.
:::An saka ranar daura auren G-Fresh da Alpha Charles
Yace tuni gwamnatin ta dasa bishiyu miliyan 1.7, a shekarar 2024, data gabata.
Sannan ya bayar da tabbacin cewa a wannan shekarar ma’aikatar muhallin zata ninka adadin bishiyun da aka dasa a cikin wannan shekara ta 2025.