Mayakan Boko Haram sun kaiwa sojojin Nigeria harin ramuwar gayya

0
59
Sojoji
Sojoji

Mayakan Boko Haram masu biyayye ga bangaren ISWAP, sun kai hari kan sojojin Nigeria dake yankin Sabon Gari a karamar hukumar Damboa, ta jihar Borno, inda suka budewa sojojin wuta da manyan makamai a ranar 4 ga watan da muke ciki.

Sai dai a yau shalkwatar tsaron kasa ta fitar da wata sanarwa mai nuni da cewa harin da Boko Haram takai na ramuwar gayya ne, sakamakon kisan da sojoji suka yiwa daya daga cikin kwamandojin kungiyar.

:::ICPC ta kai karar tsohon gwamnan Kaduna El-Rufa’i akan zargin rashawa

Daraktan yaɗa labaran shalkwatar, Manjo Janar Edward Buba, ya ce sojojin da ke komawa sansanin su daga sintirin da suke yi ne suka shammaci mayaƙan a lokacin da suke shirin ƙaddamar da harin.

Buba, yace cikin hanzari jami’an tsaron sun samu dauki daga yan banga da sauran karin wasu jami’ai wanda haka yasa cikin karamin lokaci aka samu nasara akan yan ta’addan.

Shalkwatar tsaron ta kara da cewa mayakan sun kuma dasa wani bom wanda yayi sanadiyyar jikkatar daya daga cikin kwamandojin dake aikin tsaro na sa kai, sannan bayan haka an kwato makamai daga hannun mayakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here