Shugaban NNPCL ya nemi yafiyar wadanda ya batawa rai

0
64

Shugaban kamfanin mai na kasa NNPCL, Mele Kyari, yace a baya ya kasance almajiri mai daukar karatun addinin Muslinci a tsangaya wanda daga bisani Allah ya daga darajar sa zuwa shugaban kamfanin.

Kyari, ya bayyana hakan cikin sakon murnar cikar sa shekaru 60, a duniya, wanda ya wallafa hakan a shafin sa na X.

Yace dole ne ya mika godiyar sa ga mahaliccin sa wanda ya bashi damar zama shugaban kamfanin makamashin da yafi kowanne girma a fadin Afrika.

:::Mayakan Boko Haram sun kaiwa sojojin Nigeria harin ramuwar gayya

Kyari ya ce yana godiya ga tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ma Najeriya baki daya bisa wannan damar da ya samu.

Yace tabbas ya fuskanci kalubale kafin ya samu nasarar kaiwa matakin da yake kai a halin yanzu.

Ya ce yanzu ya ƙara samun ƙarfin gwiwar hidimta wa ƙasarsa, sannan ya yi godiya da malamansa na tsangaya da na boko da sauran ƴan uwa da abokan arziki, tare da neman yafiya ga duk waɗanda ya saɓawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here