Gwamnatin Chadi ta sanar da daƙile wani harin da mayaƙa ɗauke da muggan makamai suka kaiwa fadar shugaban ƙasar da ke babban birnin kasar N’Djamena a yammacin jiya Laraba.
Kakakin gwamnatin Chadi Abderaman Koulamallah ya ce mahara 24 ne suka kai harin inda dakarun Sojin ƙasar suka kashe 18 daga cikinsu, sannan aka hallaka sojan Chadi, 1.
:::Tinubu yayi ta’aziyyar sojojin Nigeria da Boko Haram ta kashe
Koulamallah ya ce, mutane 9 sun jikkata 6 daga bangaren maharan sai 3 daga bangaren sojojin.
Harin na zuwa a dai dai lokacin da ministan harkokin wajen China Wang Yi ke ziyarar aiki a Chadin, kuma jim kaɗan bayan ganawarsa da shugaba Mahamat Idris Deby wanda ke cikin fadar lokacin faruwar harin.
A shekarar 2021 ne Mahamat Deby ya ƙarbi ragamar ƙasara matsayin shugaban riƙon ƙwarya bayan mutuwar mahaifinsa a lokacin yakar yan ta’adda.