Babban hafsan sojin Nigeria ya sanar da hanyoyin samun kudin kungiyar Boko Haram

0
41

Babban hafsan sojin Nigeria Christopher Musa, yace daga kasashen waje kungiyar yan ta’addan Boko Haram, ke samun taimakon kudade da horo ga jamia’n su, inda yace akwai bukatar majalisar dinkin duniya ta binciko hanyoyin da mayakan ke samun tallafi daga wajen Nigeria.

Christopher Musa, ya bayyana hakan a lokacin da kafar yada labarai ta Aljazeera, ke tattaunawa dashi akan sha’anin tsaro a Nigeria.

:::An kashe mutane 18 da suka kaiwa fadar shugaban kasar Chadi hari

Musa, yace akwai ayar tambaya akan yadda Boko Haram, ta kwashe shekaru 16, tana aiwatar da ayyukanta a Nigeria, inda yace tabbas akwai manakisar kasashen waje a cikin ayyukan ta’addancin na Boko Haram.

Ya ce a cikin mafi yawan mayaƙan Boko Haram da sojoji ke kamawa ana samun su da kuɗaɗen manyan ƙasashen duniya, wanda hakan ke nuna alamar ƙasashen duniya na da hannu a ayyukan ƙungiyar.

Yace kamata yayi Majalisar dinkin duniya su yi bincike kan sabuwar dabarar da ƙungiyar ta ɓullo da ita ta amfani da jirage marasa matuƙa wajen yin leƙen asiri karin su kai wa jami’an tsaro hari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here